Tuesday, 18 July 2017

Wannan hoton na Rahama Sadau yaja hankulan mutane sosai

Jarumar fim din hausa da aka dakatar, Rahama Sadau kenan tare da jarumin fim din turanci daga kudancin kasar nan, Desmond Elloit a cikin wani fim din turanci da suka fito tare me suna TaTu, yanayin shiga da Rahama tayi a wannan hoto da kuma yanda wannan jarumi ya riketa yasa hotonnan ya dauki hankulan mutane.

Dandalin shafin Instagram na Kannywoodxclusive ya saka wannan hoto, kuma da dama wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto, addu'a suka yiwa Rahama cewa, Allah ya shiryeta".

Hotunan ra'ayoyin da mutane suka bayyana akan wannan hoton.

No comments:

Post a Comment