Saturday, 29 July 2017

Wannan hoton yaja hankulan mutane

Wannan hoton yaja hankulan mutane sosai a shafukan sada zumunta da muhawara, idan ka kalli hoton kallon farko zakaga alamar mutumne yake sallah wani kuma yana tsaye yamai inuwa da kwali, kuma an danganta hoton dacewa an daukeshine a masallacin kudus dake kasar Isra'ila. Cikin wadanda sukayi sharhi akan wannan hoto wasu sun yarda cewa sallahce mutumin yake, wasu kuma sunce an hada hotonne kawai domin jan hankulan mutane, saboda idan ka duba da kyau zakaga akwai takalmi a kafar mutumin dake duke kamar yana ruku'u, wasu ma sunce mutumin ba musulmi bane.

No comments:

Post a Comment