Monday, 31 July 2017

Wannnan hoton yaja hankulan mutane

Wannan hoton gunkin da aka saba ganine a kofofin kotunan kasarnan ne, zakaga gunkin rike da wuka a hannu daya, sannan dayan hannun kaga ma'auni, wanda suke cewa wai shaidace ta adalci, kuma wannan gunkin ya samo asaline daga daya daga cikin gunkunan da girkawa suke bautawa wadda ke da suna "Justitia", to wani abu daya dauki hankulan mutane dangane da wannan hoton shine irin yanda gunkin ya kusa faduwa kasa, yanda har saida aka tokareshi da icce.

Da yawa da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto sunce alamar cewa sashin shari'a na kasarnan yana da matsala, ya kusa durkushewa kenan, saboda babu adalci a tattare dashi.

No comments:

Post a Comment