Monday, 17 July 2017

Ya cigaba da nuna mata soyayya duk da wuta ta canja mata kamanni

Wadannan masoya labarin su yana da taba zuciya, Namijin sunanshi Micheal ita kuma macen sunanta Turia, sun fara soyayya tun a makaranta, koda yake shi Micheal ne ya nunamata soyayya lokacin amma ita tana kallonshine a matsayin abokin data shaku dashi kawai amma ba soyayyaba.

Sun kammala makaranta Micheal ya zama dan sanda ita kuma ta zama injiyar hakar ma'adanai, a lokacin soyayyarsu ta fara yin karfi, Turia ta amince dashi a matsayin saurayinta. Wata rana da dukansu bazasu taba mantawa da itaba gobara ta kama gida a lokacin Turia na ciki kuma ta kasa samun hanyar fita, Allah ya kaddara bata mutuba amma ta kone halittarta gaba daya ta canja.Haka Micheal yazo ya rika zama da ita a asibiti lokacin bata san inda kanta yakeba, baya zuwa ko'ina, a karshema ya ajiye aikinshi saboda ya samu lokacin kula da ita dakyau. Jikinta ya kone kamanninta sun canja amma ko kadan irin son da yakemata be canja ba a zuciyarshi, kai asalima kamin ta farfado tasan inda kanta yake Micheal yaje ya samo zoben alkawarin aure ya yiwa kanshi alkawarin saiya aureta.

Bayan farfadowarta taga irin hidimar da yakeyi da ita kuma ta samu labarin cewa harya ajiye aikinshi, saita nuna damuwa tacemai ya kyaleta tunda dai ga irin yanda rayuwarta ta koma yaje ya samu wata sucigaba da rayuwa me dadi ta farinciki.

Micheal yace sam bazai iyaba domin shi idan bada itaba bazai iya rayuwa da kowace mace ba,, Turia taja shima yaja ya cije akan bakanshi taga tabbas da gaske yake bafa zai kyaletaba.

Saita hakura sukaci gaba da zama a haka, Turia tace amma a lokacin data fara samun kanta, babban abinda ya fado mata arai fiye da komai shine saurayinta Micheal, ta rika tunanin shikenan ta rasashi zai barta yaje ya samu wata sabuwar Budurwa, tace amma dataga yanda siyayyarshi a gareta bata canjaba abin ya bata mamaki kuma tasan cewa ya mata abinda bazata taba iya biyanshiba a har ta mutu.

Allah sarki irin wannan bawan Allah basu da yawa a Duniya.

No comments:

Post a Comment