Wednesday, 12 July 2017

Ya guntulewa matarshi yatsunta saboda tana zuwa makaranta

Wani mutum dan kasar Bangladash ya guntulewa matarshi yatsunta saboda ta shiga makarantar boko ba tare da  izininshiba, mutumin wanda ake kira da suna Rafiqul Islam ya gano cewa matar tashi tana zuwa makarantane duk da cewa ya gargadeta a baya da idandai tanason zaman lafiya ta guji makarantar idan ba hakaba zai dauki mummunan mataki akanta.

Bayan daya gano tana zuwa makaranta inda ta fara karatun digiri sai ya sameta a gida yace mata tazo akwai wata kyauta dazai bata, ya dauremata ido ya kuma kullemata baki ya kamo hannunta ya guntulemata 'yan yatsu, rahotanni sunce daya daga cikin 'yan uwanshi sun kwashe 'yan yatsun suka zubar dasu abola, wai dan kadama aje asibiti likita ya mayar mata dasu.A Yanzu dai Rafiqul Islam yana hannun 'yan sanda inda tuni harya amsa laifinshi, kuma masu fafutukar kare hakkin jama'a sun fara yin kira da'a yankemai hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.


No comments:

Post a Comment