Saturday, 29 July 2017

Ya kamu da soyayya da motarshi har yana jima'ai da ita

Wani mutum me suna Darius Monty daga kasar Ingila ya kamu da soyayyar motarshi wadda har takai ga yana jima'ai da ita dan biyan bukata kamar yanda ya bayyana.

Mutumin wanda ya sayi motar kirar Jaguar, yace yaje wajen wanketane, yana gogewa da tsumma sai yaji wata irin sha'awa da bai taba jin irintaba ta ratsamai jiki, abin ya bashi mamaki ta yanda karfe zai bashi irin wannan sha'awa dayaji.

Bayan ya koma gidane, dayake yana da budurwa, sai yaji ya kasa nutsuwa, amma be gayawa budurwar tashiba abinda ke faruwa, sai yamata karyar ya manta wani abu a cikin motarshi, ya koma dakin ajiye motar anan ne fa har saida yayi jima'i da motar kamar yanda ya bayyana.


Darius yace bayan faruwar hakan sai yaji duk baiji dadiba, jikinshi yayi sanyi, ya rika tambayar kanshi wai menene ya aikata haka? 

Can dai ya yanke shawarar yin bincike a yanar gizo dan ya gano cewa ko akwai wasu masu irin wannan halayya tashi a Duniya? aikuwa yana bincikawa sai yaga akwai masu irin wannan dabi'ar tashi da ba kasafai take faruwa ba, ita wannan dabi'a ana kiranta da suna mechanophilia, a turance wadda kesa mutune wasu su kamu da soyayya da babur dinsu wasu, mota, wasu jirgin sama. dadai sauran abubuwan da basu da rai.

Da Darius ya gano haka sai yaji hankalinshi ya kwanta, kuma ya daina boye-boye, ya fito fili ya baiwa budurwarshi labarin abinda ya faru, nan take kuwa ta kama gabanta inda ta gayamai yaje ya nemi likitan mahaukata ya dubashi domin yayi gamo.

Haka kuma ya gayawa abokanshi abinda ke faruwa, nan suma sukamai dariya, amma da sukaga da gaske yake sai sukacemai wannan abu nashi na musamman ne.

Darius yace yasan motar bazata iya sonshiba, domin bata da rai, amma shi besan yanda wannan abu ya faruba kawai yana sonta, domin tsabar soyayyar da yakewa motar yace ya daina hawa titi da ita, ya killaceta saidai kawai yaje su gana.

Haka kuma Darius yace yana saran zai samu mata ya aura har su tara iyali, amma fa sai idan ta amince da soyayyarshi da motarshi, wani likitan fahimtar halayyar dan Adam yace babu wata matsala akan abinda ke faruwa da Darius domin soyayyar tashi da motarshi bata sa ya zautu ba, yasan cewa motar bata da rai amma yana sonta a haka to don wani yace hakan bai mai ba ba wani abu bane.
jaridar mirror ta kasar Ingilace ta wallafa wannan labari.

No comments:

Post a Comment