Wednesday, 19 July 2017

Ya kashe Diyarshi Saboda tanaso ta auri musulmi

Wani mutum dan kasar Isra'ila ya kashe diyarshi ta hanyar caka mata wuka saboda ta nace sai ta auri saurayinta musulmi. Mahaifinnata wanda shi ba musulmi bane yayi kokarin rabata da saurayin nata amma yarinyar fur taki yarda, tace ita tana son shi.

Saurayin nata yana kulle a gidan yari kuma tayi alkawarin zata musulunta idan ya fito daga gidan yarin yanda daga karshe sai suyi aure, hakan ya kara hasala babanta me suna Sami, ya rika mata dukan rashin imani, kamar jaka, dataga abin nashi ba wanda zata iya jurewa bane, saita gudu ta tafi gidan mahaifiyar saurayinta ta zauna acan.Yarinyar ta rika kiran kawayenta tana gayamusu cewa mahaifinta na kokarin kasheta, abin yana bata mamaki.

Mahaifin nata ya kasa jurewa ya bita can gidan mahaifiyar saurayin nata ya dawo da ita gida, daga nanne sai gawarta aka gani a cikin gidan da raunin dake nuna alamar an caccaka mata wuka a jiki.

Damadai 'yan sanda na zargin Sami da mu'amala da gurbatattun kwayoyi masu kawar da hankali, kuma an saka mishi wata na'ura me daukar duk wani abu dake faruwa a gidanshi, kuma ta hakane aka kamashi.

Yanzu dai shi Sami da matarshi da kawun yarinyar suna hannun 'yan sanda.

Amma Sami ya musanta wannan zarge-zarge da ake yi masa.

No comments:

Post a Comment