Tuesday, 18 July 2017

Yanayin rayuwar kwaron filfilo

Akwai kalolin kwaron malam budemana littafi ko kuma filfilo kamar yanda ake kiranshi, suna da ban sha'awa zaka gansu suna tashi daga wannan fure zuwa wancan kusan duk mun sansu, amma muna ganinsu ne kawai ba tare da sanin ainihin yanda halittar jikinsu yakeba, ga kadan daga wasu bayanai masu birgewa da ban mamaki akan kwaron filfilo/malam budemana littafi.

ZAKA IYA GANIN KOMAI TA CIKIN FIFFIKEN KWARON MALAM BUDEMANA LITTAFI(wato abinnan da ake kira transparent da turanci).

Abin zai baka mamaki koh? To amma da gaskene, zakaga cewa fiffiken malam budemana littafi yana da kaloli daban-daban,  wasu kwayoyin halittane ke fitowa akan fiffiken nashi wadanda idan rana ta haskasu saisu rika bayar da kalar da muke gani a jikin fiffiken, amma idan Filfilo ya fara tsufa wadannnn kwayoyin halitta suna kakkabewa subar ainihin fiffiken wanda zaka iya ganin komai ta cikinshi.


DA KAFA KWARON FILFILO KE DANDANON ABINCI:
Idan kwaron filfilo/malam budemana littafi ya sauka akan fure ko ganye yana amfani da kafarshine wajen gane dandanon furen, yaji ko irin wanda yake da bukatar cine.

Haka itama ta macen filfilo tana amfani da kafarta domin gane ganyen daya kamata ta saka kwayayenta akai.

KWARON FILFILO BAYA TAUNA ABINCI, SAIDAI YA SHA ABU ME RUWA-RUWA:

Yanayin bakin kwaron filfilo Allah ya halicceshine yanda saidai ya tsotsi abinci kawai amma bazai iya taunashiba, yana da wani dan karamin bututu a bakinshi wanda da shine yake amfani yana zukar ruwan furen da yake son sha.

IDAN YAKAI MATSAYIN CIKAKKEN HALITTA, KWARON FILFILO SAI YA HADA BAKINSHI YANDA ZAI RIKA SAMUN TSOTSAR ABINCI:

Da zarar yakai matsayin da zai fara cin abinci, kwaron filfilo yana yin kokarin hada bakinshi ya zama bututu don ya samu ya rika tsotsar abinci, bakin nashi yana zama kashi biyune to sai ya gwada wannnene ya kamata ya rika amfani dashi wajen cin abinci.

KWARON FILFILO YANA BUKATAR CIN ABINCI DANAB-DABAN:

Namijin kwaron filfilo, bayan ruwan fure da yake zuka, yana kuma zukar irin ruwan dake kasa, musamman wanda akayi ruwan sama yadan kwanta, domin ya samu wasu sinadaran abinci wanda suke komawa ruwan maniyi, wanda dashine idan ya sadu da tamacen filfilo zata samu kwayaye ta haihu.


IDAN SANYI YAYI YAWA KWARON MALAM BUDEMANA LITTAFI BAI IYA TASHI SAMA:

Akwai yanayin zafin jiki da kwaron malam budemana littafi ke bukata kamin ya iya taahi sama, idan kuwa bai samu wannan yanayin zafin jikinba koda kuwa wata halitta tazo zata cutar dashi ko kuma ta kasheahi bazai iya guduwaba, haka kuma bazai iya tafiya neman abinci ba. Haka kuma akwai yanayin zafin jikin da idan yamai yawa ahima baya iya tashi

JARIRIN KWARON MALAM BUDEMANA LITTAFI BAYA IYA TASHI SAMA:

Bayan an haifeshi, kwaron filfilo yana rayuwa zuwa matsayi matsayi kamin ya samu fuffuke ya fito a jikinshi wanda zai bashi damar tashi sama, a lokacin da fuffuken ya fito, zai zama kamar ledane ko kuma balam-balam, wanda sai filfilon ya ya watsomai wani ruwa daga jikinshi kamin ya bude gaba daya, yakai daidai ainihin girmanshi, sannan ya fara gwada tashi.

MAFI AKASARI KWARON FILFILO YANA RAYUWAR TSAWON SATI BIYU ZUWA HUDUNE A DUNIYA:

Kwaron filfilo baya dadewa a Duniya, yawanci sati biyu zuwa hudu yakeyi, abubuwa biyu yake mayar da hankali akai bayan yakai matsayin cikakkiyar halitta, yana mayar da hankali kan cin abinci da jima'i, saidai akwai wasu kadan da suke kaiwa watanni 9.

KWARON FILFILO  BAYA IYA HANGO ABU ME NISA:

Idan abu yayi nisan kafa goma zuwa shabiyu kwaron filfilo baya iya hangoshi da kayu, zai rika mai dishidshi, amma a nisan dabe kai hakaba kwaron filfilo yana iya hango kaloli daban-daban har da wadanda idon mutum baya iya gani, haka kuma yana hango irin abincin dayake sonci da kuma neman abokiyar yin tarayyar jima'i.

KWARON FILFILO YANA AMFANI DA WASU DABARU WAJEN GUJEWA MASU CINYESHI:

Filfilo bashi da wayau sosai, saboda haka sauran gwaruka na samun wallenshi wajen cinyeshi cikin sauki, amma duk da haka akwai wasu dabaru da yake amfani dasu wajen buya, wani filfilon idan ya hango wani gwaron dazai iya cinyeshi ya tukaroshi, yakan nade fuka fukanshi ya saje da irin furen da yake kanshi, wani kuma yana karawa kalar jikinshi haskene yanda duk inda ya sauka za'a san ya sauka, dabarar itace sauran kwaruka sunsan cewa idan sukaci kwaro wanda keda haske sosai yana zamar musu guba.

No comments:

Post a Comment