Sunday, 30 July 2017

Yanda wannan me daukar daukar hoton ke sanye da takalmi a cikin masallacin harami ya jawo cece-kuce

Wannan hoton ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, dalili kuwa shine, wannan me daukar hoton da aka ganshi sanye da takalmi a masallacin harami na makka, inda ba'a bari a shiga da takalmi, da yawa wadanda sukayi sharhi akan wannan hoton sun rika tambayar "meyasa wannan me daukar hoton ke sanye da takalmi a cikin masallaci?".

Wasu dai cewa sukayi wannan hoton hadashi akayi, domin babu ta yanda za'ayi a bar mutum ya shiga masallacin harami da takali a kafarshi, baza'a iya cewa ba hadin hotobane wannan, amma yayi matukar kama da cewa gaskene, domin babu wata alama dake nuna cewa anwa hoton kwaskwarima, in kuwa hadin hotonne to gaskiya wanda yayishi kwararrene ba kadan ba.

No comments:

Post a Comment