Friday, 28 July 2017

Za'a baiwa Fursunonin kasar Jamaika damar tarawa da iyalansu

Gwamnatin kasar Jamaika zata baiwa mazauna gidan yari damar tarawa da iyalansu, Ministan tsaron cikin gida na kasar ne ya bayyana haka, yace, ya kamata a rika yiwa fursunonin kula irin ta mutane.

Haka kuma ya kara da cewa masu tambayar cewa meyasa za'ayi haka, ya kamata su san cewa su kiristane, kuma kirista ana bukatar ya yiwa kowane irin mutum adalci, haka kuma yace baiwa fursunonin damar tarawa da iyalinsu zai kara kusanta tsakaninsu, kuma zai kawar da hankulansu akan wasu munanan ayyukan ashsha da ake aikatawa a gidan yari.Kungiyoyin kare hakkin bil'adma na kasar sunyi na'am da wannan sabon tsari. Wannan labarin yaja hankulan mutane da dama a shafukan sada zumunta.

No comments:

Post a Comment