Wednesday, 19 July 2017

Za'a haifawa Cristiano Ronaldo da na hudu

Tauraron dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo zai samu yaron gaba da fatiha na hudu wanda ake tsammanin budurwarshi zata haifamishi, an dai ga budurwar tashi da alamar cikine shine 'yan jarida suka tambayeshi ko gaskiyane budurwartashi nada ciki?, Cristiano ya tabbatar da hakan.

Koda a watan daya gabata wata, uwar aro ta haifawa Cristiano 'yan biyu wanda a yanzu yace yana koyon yanda ake saka musu fanfas, haka kuma Cristiano yana da yaro dan shekaru bakwai wanda shima wata uwar aroce ta haifawa mishi shi.

No comments:

Post a Comment