Tuesday, 18 July 2017

Ziyarar Malala Yusufzai Najeriya: gaisuwar da tayi da Osinbajo taja hankula

'Yar rajin kare hakkin 'yan mata musamman kanana, wajen ganin sun samu ilimi yanda ya kamata, Malala Yusuf Zai ta kawo ziyarar bangirma ga mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, wannan ne karo na  biyu da Malala take kawo ziyara Najeriya, Malala dai ta samu daukaka a Duniyane bayan 'yan yakin Taliban sun harbeta akai saboda zuwa makarantar boko, wanda cikin ikon Allah bata mutuba ta warke, kuma bayan ta samu sauki aka tambayeta game da wadanda suka mata danyen aikin sai tace ta yafe musu, wadannan dalilai yasa ta samu kyautar zaman lafiya ta Duniya, wadda a yanzu itace mafi kankancin shekaru data taba samun wannan kyauta.
Saidai a wannan ziyarar tata masu sharhi a shafukan sada zumunta da muhawara sun mayar da hankali kan irin gaisuwar datayi da mukaddashin shugaban kasa, Osinbajo, waau dai suna ganin cewa a matsayinta na musulma be kamata ta gaisa da shi ba domin hakan ya sabawa koyarwar addininta.

No comments:

Post a Comment