Saturday, 5 August 2017

Adam A. Zango ya koma Noma

Jarumin fim din hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan a wannan hoto nashi daya saka a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, Hoton dai ya nuna Adamun a cikin wata gonane kuma ya rubuta "Alhamdulillahi Noma tushen arziki" , ga dukkan alamu gonar ta Adamunce, duk da cewa bai bayyana hakan ba, amma masoyanshi da dama sunyi mamakin ganinshi a gona, inda suka rika tambayar, wai dama kana nomane?

A sati biyu da suka gabata cikin wata hira da Adam A. Zango yayi da kafar watsa labarai ta bbchausa ya bayyana cewa, masu harkar danyen maine kawai sukafi samun kudi fiye da 'yan fim a kasarnan.Muna taya Adamu farin ciki da fatan alheri da kama sana'ar noma da yayi.
Ga wasu daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana akan wannan batu.
No comments:

Post a Comment