Sunday, 6 August 2017

Akwai bukatar a taimakawa wannan yaron yacigaba da karatu saboda hazakar daya nuna


Shitu Abdullahi Dan Asalin Karamar Hukumar Mallammadori A Jihar Jigawa, Shine Ya fi Kowanne Dalibi Cin Jarabawar WAEC Da JAMB A Jihar Jigawa.

Shitu Ya Kamamala Makarantar 'Gifted and Talented' Bamaina A Wannan Shekarar Ta 2017. Inda Ya Samu Distention A Dukkan Darusa 9 Na Jarabawar WAEC, Sannan Ya Sami Maki 306 A Jarabawar JAMB.Sai Dai Babban Abun Bakin Ciki Iyayen Dalibin Ba su Da Halin Da Za su Iya Tura Dan Nasu Jami'a.

Akwai Bukatar Gwamnati Ko Masu Hannu Da Shuni Dasu Rinka Taimakawa Hazikan Yara Kamar Shitu Abdullahi, Domin Al'umma Su Amfana Da Ilimi Da Allah Ya Ba su.
rariya.

No comments:

Post a Comment