Saturday, 5 August 2017

An sawa wani layi sunan Muhammad Indimi a jihar Gombe

An sakawa wani layi a jihar Gombe sunan hamshakin attajiri, sirikin shugaban kasa, Muhammad Indimi. Muhammad Indimin yaje da kanshi dan bude wannan layi, ya kuma nuna farinciki da wannan karramawa da akamishi. Wannan karranawa da aka yiwa Muhammad Indimi tazo daidai da ranar da yake cika shekaru saba'in da haihuwa a Duniya, Muna tayashi murnar zagayowar ranar haihuwarshi da kuma wannan karramawa daya samu.
Gwamnan Borno, Khashim Shattima da Gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo da sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar, sun taya Muhammad Indimi murna.
Karin hoto.

No comments:

Post a Comment