Sunday, 6 August 2017

An tserewa wanda yafi kowa gudu a Duniya, Usain Bolt a tserenshi na karshe

Tauraron tserennan dan kasar Jamaica, wanda yafi kowa gudu a Duniya, kamar yanda ake gayamai, wato Usain Bolt yayi tserenshi na karshe, kuma wani abinda yaba mutane mamaki shine baizo na daya ba, na uku yazo, wani ba'amurkene wanda dama shine kusan a koda yaushe yake kwatanta yin gogayya da Usain Bolt din wato Justin Gatlinne yazo na daya. To saidai duk da Usain Bolt bezo na daya ba a tseren, 'yan kallo sunyita kiran sunanshi, haka kuma shima Gatlin ya durkusa gaban Usain Bolt wanda hakan yake nuna alamar girmamawa, hakan dai baya rasa nasaba da cewa wannan tseren bankwanane Usain Bolt yayi. Kuma shi Gatlin an taba samunshi da amfani da kwayoyi masu karamai kuzari a shekarun baya, amma aka yafemai yazo yaci gaba da wasa.

Ana saran wannan tsere da Usain yayi a jiya a birnin landan, shine na karshe wanda daga shi zaiyi ritaya ya daina gudu yaje ya huta.Mutane da dama a sassa daban-daban na Duniya sunyita rubuta sakonnin dake nuna alhinin bankwana da Usain Bolt a tsere, kuma wani abu da aka rika mainaitawa, shine kamin ayi wannan tseren an tambayi Usain Bolt ya yake son tserenshi na karshe ya kasance? Sai yace yana so yayi nasara saboda a rika tunawa dashi a matsayin wanda ya zama gagara gasa, wanda ba'a iya dokeshi indai a fannin tserene, to amma sai gashi abin yazomai da gaddama.


Amma duk da haka Duniyar tsere bazata taba mantawa da Usain Bolt ba domin a tsawon tseren da yayi ba'a taba samunshi da amfani da kowane irin maganin kara kuzariba, haka kuma Shine ya rike kambun tseren maza na mita dari da dari biyu na Olamfic sau uku a jere ba tare da an samu wanda ya dokeshiba, hakan yasa ya zamo wani abin kwatance wanda ake ganin ya kawo cigaba a harkar tsere.

No comments:

Post a Comment