Tuesday, 1 August 2017

Budurwa ta amshi addinin musulunci, amma iyayenta suna da ja

Athira, the missing Hindu girl, returns as Ayesha after converting to Islam
Wannan yarinyar 'yar kasar Indiya me suna Athira, wadda ita da iyayenta mabiya addini Hindune, ta bar gidan iyayennata domin taje ta koyi yadda ake yin addinin musulunci saboda yana bata sha'awa. A ranar goma ga watan daya gabatane Athira ta bar gidan iyayenta, ta rubuta musu wasikar cewa ta tafi domin taje ta koyi yanda ake yin addinin musulunci, saboda addinin yana birgeta.

Amma iyayen nata basu gamsu da wannan wasikar data bariba, sai suka fara tunanin ko zata shiga kungiyar masu jihadine, sai suka kai kara wajen hukuma cewa diyarsu ta bata, 'yan sanda suka shiga nema ba dare ba rana, ita kuwa Athira tana can tuni harta gama nazarin addinin musulunci kuma Allah ya haskaka mata zuciyarta, harta karbi kalmar shahada kuma ta canja suna zuwa A'isha.
Koda taji labarin ana nemanta da sunan cewa wai ta bata, saita fito ta kai kanta gurin hukuma, a lokacin tuni har magana taje kotu, Athira ta bayyanawa alkali tana son iyayenta kuma babu wanda ya tilasta mata komawa addinin musulunci, zabintane, kuma idan iyayennata sun amince tacigaba da neman ilimin addini da kuma zama a matsayin musulma to zata bisu, amma idan sunce dole saita koma addinin Hindu to zata kama gabanta.

Alkali ya bayyana cewa tundadai Athira tazama cikakken mutum, ba yarinya bace to tana da damar zabin addinin da takeso. Amma iyayen basu gamsu da wannan hukunciba, kuma sun daukaka kara zuwa babbabr kotu, amma acanma hukuncin be canjaba, alkalin kotun yace Athira tana da damar yin addinin da takeso, haka nan suka hakura suka koma gida da diyarsu, amma alkalin yace idan sunga wani abu da basu fahimtaba a tattare da dabi'un A'isha, to zasu iya karan hukuma domin ta kawo musu dauki.
Kafar watsa labari ta asianet newsable ce ta wallafa wannan labari.

1 comment:

  1. Lallai. Gaskiya ta zabi halaka, adinin sha jini. Blood sucking religion. Terrorist

    ReplyDelete