Saturday, 5 August 2017

Cikakken bayani kan cinikin Neymar daga Barcelona zuwa PSG

Labarin komawar tauraron dan wasan kwallon kafa, Neymar Club din PSG daga Barcelona yaja hankulan mutane sosai a wannan satin daga gabata, babban abin da yafi daukar hankali akan labarin shine zunzurutun kudin da aka sawa Neymar din da suka kai sama da fam miliyan dari biyu, wanda hakan yasa ya zama dan kwallo mafi tsada a Duniya, Barcelona ta samu riba sosai da Neymar domin kuwa kudinnan da aka sayeshi yanzu sun ninka wanda Barca din ta sayoshi sau uku da rabi. A dadai kamin Neymar, dan wasan Manchester United, Paul Pogba ne yafi tsada wanda a shekarar data gabata aka sayeshi akan Fam miliyan tamanin da tara, to amma gashi Neymar ya ninkashi fiye da sau biyu a tsada.

Haka kuma wani abu daya kara jan hankali akan wannan ciniki shine yanda Club din PSG ya biya kudin Neymar din a dunkule ba bashi, da farko dai hukumar wasannin kwallon kafa na Laliga tace bata amince da wannan ciniki ba, amma awa daya bayan wannan sanarwar sai gashi PSG ta biya Barcelona kudin Neymar a dunkule, haka shi kanshi club din Bercelona an ruwaito cewa yayi mamakin biyan kudin da PSG tayi yanda har saida ya bukaci hukumar kula da kwallon zakarun turai UEFA ta bincika yanda PSG din ta biya kudin a dunkule, anya bata babu wani magu-magu?To saidai wasu masu sharhi sun bayyana cewa biyan kudin da PSG tayi ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da wanda ke da club din, larabawane 'yan kasar Qatar da suke cikin harkar mai dumu-dumu kuma suna da manyan kudi.

Neymar dai ya saka hannu a kwantirakin shekaru biyar a PSG, wato zai kare nan da shekarar 2022, kuma anyi kintacen za'a biyashi zunzurutun kudin albashi da alawus-alawus da suka kai dala miliyan dari uku da hamsin, kamin a fitar da haraji, a tsawon wannan lokaci. Hakan yasa ya shiga gaban Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a karbar albashi.

Amma Neymar din yace kudin da aka sayeshi bafa suyi tsadaba, kuma yana mamakin masu cewa wai saboda kudine ya koma PSG din.

Hakanan akwai rahotannin da suka rika yawo dake cewa baban Nymar din bai goyi bayan tafiyarshi PSG ba, yafi so ya tsaya a Barcelona, amma Neymar din ya roki babanshi daya goyamai baya domin shikam yana son tafiya
A wannan hoton Neymar ne da Pique suke bankwana, da alama akwai kyakyawar alaka a tsakaninsu, Neymar yace ya gargadi Pique a baya da ya daina gayawa mutane cewa yana nan a Barcelona bazai koma PSG ba.

No comments:

Post a Comment