Friday, 4 August 2017

"Da ana canjen lafiya, da naba Baba Buhari tawa">>Sa'ed Nagudu

Shahararren mawakin hausarnan, Sa'ed Nagudu ya bayyana cewa a cikin shuwagabannin Najeriya babu wanda yafiso kamar shugaban kasa, Muhammadu Buhrai, wannan daliline yasa Sa'ed yace da ana yin canjen lafiya to tabbas daya roki Allah ya ba Baba Buhari lafiyarshi shi kuma a bashi ciwon Baba Buhari, saboda irin son da yake mishi.

Gadai abinda Sa'ed yace kamar haka"Da ana canja lafiya da na roki Allah ya cire wa Baba BUHARI cutar dake damunsa ni ya dora min, shi a ba shi lafiya ta. Sabida yadda nake son Buhari nake kaunar Baba Buhari, bana kaunar kowa haka a shugabanin Nijeriya".

rariya.

No comments:

Post a Comment