Wednesday, 2 August 2017

Hotuna masu kayatarwa daga ziyarar da Osinbajo yakai jihar Kebbi

Ziyarar mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, zuwa jihar Kebbi tayi armashi sosai, Osinbajo hadu da gamayyar gwamnonin jamiyyar APC, a jiya, talata daya ga watan Agusta, inda suka hadu a Kebbin dan kaddamar da wani kata faren kamfanin sarrafa shinkafa da gwamnan jihar ya gida, yara 'yan makaranta da matasa masu bautar kasa, kai har dama jama'ar gari sun yiwa Osibajo kyakkyawar tarba.Wannan hoton na kasa, wata tarakatar nomace da akae kerata a jihar kebbi, wadda a jiya talata aka fito da ita tare da wasu kayan aikin gona da aka kera a jihar dan nunawa jama'a.
Wannan hoton na kasa kuma Osinbajone yake duba wasu jibga-jibgan kifaye da aka kamo a argungu.


No comments:

Post a Comment