Tuesday, 1 August 2017

Kalli hotuna masu kayatarwa dake nuna cigaban garin Dubai

Wannan hoton na sama birnin dubaine, an dauki hoton ne daga saman shahararren ginin nan dayafi kowane gini tsawo a Duniya, kuma wanda kusan za'ace shine yafi daukar hankali a birnin Dubai, wata Burjil Al-Khalifa. Kamin ya samu cigaba ta hanyar danyan mai da kuma cinikin gidaje wanda yasa ya zama daya daga cikin garuruwan dake da karfin tattalin arziki a Duniya, garin Dubai ya kasance wani dan karamin gari da bashi da wani tattalin arziki na azo a gani, wanda mafi yawanci aikin kamun kifine jama'ar garin keyi.
Wannan hoton faifayen da ake amfani da sune wajen samar da wutar lantar a Dubai ta hanyar hasken rana, kuma shine irinshi mafi girma a hadaddiyar daular larabawa, haka kuma wannan wutar lantarki da ake samarwa ta hasken rana dake gari Dubai, itace mafi saukin kudi a Duniya.

Fraiministan hadaddiyar daular larabawa, Muhammad Bin Rashid Almaktoum kuma wanda shine sarkin Dubai, yana aiki tukuru wajen ganin ya bunkasa garin sosai yanda zai kasance cikin biranen Duniya da ake alfahari dasu.
Wannan hoton na sama shima wata babbar tashar samar da qutar lantarkice ta garin Dubai, ana amfani da gasne wajen samar da wutar a wannan tashar, amma rahotanni sun nuna cewa nan gaba za'a rika amfani da hasken rana a wannan tashar dan samawa birnin wutar lantarki.
Anan mutanene keta daukar hotuna daga kan ginin Burjil Al-Khalifa, dayafi kowane tsawo a Duniya, wannan hawa na dari da shirin da biyar kenan, birnin Dubai yana samun kwararar masu yawan bude ido da yawa.
Wannan hoton babban titin garin Dubai kenan da ake kira da, titin shaikh Zayed, hoton ya nuna irin yanda wutar lantarkin da babu yankewa ke karawa garin kyau da dare.
Lucalocatelliphoto.

No comments:

Post a Comment