Tuesday, 1 August 2017

Koriya ta Arewa ta razana kasar Amurka

Kasar Amurka ta kadu da wani gwajin makamai na karkashin ruwa da kasar Koriya ta Arewa ta gudanar, kamar yanda jami'an kasar Amurkar dake sa ido akan harkokin kasar Koriya ta arewa suka bayyana, koriya ta arewar tayi gwajin wani babban makami da ba'a taba tsammani ba, kuma gwajin yayi nasara.

Ana dai takun saka tsakanin kasar Amurka da kasar Koriya ta Arewa, saboda kokarin mallakar makaman kare dangi da koriya ta arewar takeyi da kuma gwaje-gwajen makamai masu linzami ba kakkautawa, kasar Amurka tana yiwa kasar Koriya kallon hadarin kaji, da ganin cewa bata isa ace ta gagaraba, amma watakila wannan gwajin makamin da koriyar tayi ya canja tunanin Amurkar.

No comments:

Post a Comment