Sunday, 6 August 2017

Maza sun fara gane muhimmancin tallafawa mata da ayyukan gida?

Allah sarki wasu mazan nada tausayi, sun fahimci irin yanda mata ke dawainiya da gida da kuma rainon 'ya 'ya shiyasa wani lokutan suke tallafa musu da rainon yara, wani namijin baidama lokacin dazai zauna yayi hira da iyalinshi, shidai neman kudi kawai ko kuma zama a majalisa, wanin kuma ganiyake idan yayi irin wannan to wai za'a rainashine, wallahi ko daya a duk lokacin da kake nunawa abokin zamanka tausayi da tallafamai wajen yin ayyukan da musamman ba muhallinka bane to tabbas akwai wata kima da daraja da kake karawa kanka a gurin wannan mutumin.
Sannan kuma yana daya daga cikin abinda zai karama shakuwa da soyayya dasu kansu 'ya 'yan naka, yanzu misali, bayan shekaru da dama bayan danka ko 'yarka ta girma, sai taga irin wadannan hotunan, yanda kake goyata tana yarinya sannan 'ya 'yanka maza sukaga irin yanda kake taya mahaifiyarsu aiki a kicin, suna sonka a matsayin mahaifinsu, amma tabbas akwai wani irin so da jin dadi dazai kara shigarsu a wannan lokaci sannan kuma hakan basu tarbiyyane a fakaice, domin suma idan sukayi aure nan gaba zasu so su yiwa matansu irin haka.Allah yasa mu dace ya kuma bamu ikon sassauto da kawunanmu kasa mu rika tallafawa abokan zamanmu.


hotuna daga dandalin Maryam Kaita.

No comments:

Post a Comment