Friday, 4 August 2017

"Na yi farin ciki kan yadda na ga Buhari ya murmure cikin sauri,">>inji Shugaban Cocin Ingila

Buhari
Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby, ya kai ziyara ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Landan.
Justin Welby ya ziyarci Shugaba Buhari ne, wanda ya kwashe kusan wata uku yana jinya a birnin Landan ranar Juma'a.
"Na yi farin ciki kan yadda na ga Buhari ya murmure cikin sauri," in ji jagoran cocin.


A baya ma dai jagoran cocin ya kai ziyara ga shugaban, lokacin da ya yi jinya a farkon shekarar nan.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar ke jinya a Ingila a shekarar 2017.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment