Wednesday, 2 August 2017

Sani Maikatanga zai dauki mutane hotuna kyauta don murnar zagayowar ranar haihuwarshi

Shahararren me daukar hotonnan, Sani Maikatanga zaiyi murnar zagayowar ranar haihuwarshi ranar shabiyar ga watan Agustannan da muke ciki, idan Allah ya kaimu, kuma saboda murnar wannan rana, Sani yace duk wanda shima ranar haihuwarshi tayi daidai da wannan rana, kuma yana zaune a garin Kano, to yazo zai daukeshi hoto kyautar Allah wata'ala. To ga wadanda suke murnar zagayowar ranar haihuwarku sai ku shirya kuyi tururuwa shagon Sani.

No comments:

Post a Comment