Sunday, 6 August 2017

Wannan hoton ya jawo cece-kuce

Kafar watsa labarai ta bbchausa ta saka wannan hoton na shugaban kasa, Muhammadu Buhari da matarshi a kusa dashi sannan da wata baiwar Allah acan ta dayan bangarenshi a shafinsu na sada zumunta da muhawara, sannan sukayi tambayar"Menene sunan wadda take tsaye kusa da shugaba Buhari banda mai dakinshi A'isha?".

Wannan tambaya da bbchausa sukayi ta jawo zazzafar muhawara tsakanin mutane, Shin wai kodan waccan din wadda ba A'ishaba tafi matsuwa kusa da Buharine a hoton ko kuwa dan saboda hoton mata da mijine, amma sai gashi wata tazo wadda mutane basu saba ganinta a tare dashi sun sakashi tsakiya?.Gadai hotunan wasu daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana akan wannn hoton.

No comments:

Post a Comment