Friday, 4 August 2017

Wasu bata gari na amfani da sunan Fati Muhammad wajen neman kudi

Wasu bata gari na amfani da sunan jarumar fim din hausa Fati Muhammad wajen bude dandali a shafin Instagram suna aikawa mutane da rokon su basu kudi da sunan jarumar, Fati tayi kira da'ayi watsi da duk wani sako da wadannan mutane ke aikawa domin bata da wata alaka dasu, suna yine domin bata mata suna.

Ga sakon da Fati ta fitar kamar haka"Alaikum Masoyana! Barkammu da Jummu'a. Ina sanar daku cewa... bani da wani account bayan wan nan, duk account din da za ku gani bayan wan nan ba nawa bane. Sukan tambayi... kudi, katin waya da sauran su, Kar ku saura re su in sun roke ku wani abu ta DM. Nagode love you all ❤️ INAIMUKU FATAN ALKHAIRI
TAKU FATI MUHAMMAD"
Ga hoton dayan shafin bogen dake amfani da sunan Fati Muhammad.

No comments:

Post a Comment