Tuesday, 1 August 2017

Wasu muhimman bayanai dangane da wayar hannu

Kullun kana taba wayar hannu, watakilama itace abinda kafi yawan tabawa a kowace rana, da za'a rabaka da ita na kwana daya, ba karamin takura zakaji ka shiga ciki ba, ga wasu bayanai dangane da wayar da kake amfani da ita a kullun.

Ka tuna karamar wayar Nokia din nan 1100?, itace abun amfanin wutar lantarki da yafi yin kasuwa a Duniya, domin an sayar da kwafin wayar har guda miliyan dari biyu da hamsin.

Ka rika kula wajen amfani da wayar ka, domin kwayoyin cutar bakateriya dake jikinta yafi yawan kwayoyin bakateriyar dake jikin hannun kora ruwa a bayi bayan biyan bukata, sau kusan goma sha tara.

Kashi casa'in cikin dari na wayoyin dake kasar Japan ruwa baya musu komai, saboda yawancin matasa a kasar na yin wanka tare da wayarsu a hannu da kuma shiga kudiddifin ninkaya da wayayoyinsu a hannu.

Wayar hannu na fitar da wasu sinadarai dake sakawa mutane ciwuka, irin su, yawan mantuwa, kasa yin bacci, ciwon kai, haka kuma sanadin wayar hannu, an samu wasu sabbin ciwuka, kamar, ringxiety, wanda ciwone da zaisa mutum ya rika jin cewa wayarshi kamar tana kuwwa(ankirashi), alhali ba kiranshi akayiba(nasan ka taba jin haka), da kuma cutar nomophobia, ita kuma wannan cutace dake sa mutum ya rika jin tsoron rabuwa da wayarshi, akwai kuma cutar telephonophobia, ita kuma wannan cutar tana sa mutum ya rika jin baison ko kuma tsoron daukar kiran waya, idan an kirashi, da kuma tsoron yin kiran waya, akwai kuma cutar frigensophobia , wadda ita kuma take sa mutum ya rika jin cewa wayarshi tana lalata mishi kwakwalwa.Masana kimiyya sun gano hanyar da mutum zai iya yin cajin wayarshi da fitsari.

Wani mutum me suna Martin Cooper ne ya fara yin kiran waya a Duniya, a shekarar 1973.

A kasar Ingila mutane na kora wayayoyin hannu guda dubu dari cikin bayi duk shekara.

Kashi saba'in cikin dari na wayoyin Duniya, kasar China ce ke kerasu.

Kashi tamanin cikin dari na mutanen Duniya nada wayar hannu.

Wayar hannu tafi kwamfuta yawa da ninki biyar a Duniya.

Wasu basu da burushin wanke baki, amma sunada wayar hannu.

Yawancin sakonnin da aka aika ta wayar hannu ana karantasune cikin mintuna uku, bayan isar su ga wanda aka aikamawa.

Masana'antar wayar hannu tafi kowace masana'anta cigaba a Duniya.

Wayar da tafi kowace waya tsada a Duniya, itace iphone 5 black diamond, kudin wayar yakai dalar amurka miliyan goma sha biyar.

Wasu mutane nada wayar hannu amma basu da bandaki.

A kasar Finland, akwai wani wasa na musamman da akeyi da mutane zasu taru suyita jefa wayoyinsu a dandan kasa.

Ana samun mutane na mutuwa wajen daukar kansu hoto(wato selfie).No comments:

Post a Comment