Sunday, 6 August 2017

Yanda wasu sojoji ke son komawa ma'aikatan mata

Wani abu dake faruwa a cikin al'umma dabai dace a bari ya cigaba da faruwa ba saboda cigaba da faruwarshi akwai matsalar dazai iya jawowa nan gaba, to amma matsalar itace ta yaya za'a tsayar da wannan abu?, domin masu dokar baccine suke neman su bige da gyangyadi.

Akwai wasu sojojin kasarnan, manya da kananansu, da farar hula, musamman mata ke amfani dasu wajen wulakanta jama'a ko kuma cimma wani burinsu akan wani mutum, zakaga da an samu wata rashin fahimta, maimakon a kira dan sanda wanda shine yafi kusa da al'umma kuma aikin sasantawa yafi dacewa dashi sai a zarce ayi wajen sojoji ko kumama a kirasu a waya.

Sati kusan biyu da suka gabata naje ofishin wani Major, muna magana dashi sai wata mata ta bugomai waya tana gayamai cewa "itafa mutuminnan yaki bata kudinta kuma ta tabbata cewa yana da kudin" sai sojannan yake cemata to kawai taje inda mutumin yake indai ta ganshi kawai ta kirashi a waya, zai tura sojoji su tafi dashi, anan nayi karambani nace ranka ya dade ba gurin 'yan sanda ya kamata takai wannan karan ba? sai yace ai mutanen ne wasu idan ba sunga uwar bariba basa yin abinda ya kamata, damadai karambani nayi, danaji haka sai nayi shiru, amma abin yacigaba da damuna a zuciya.Haka kuma a layinmu na dawo da yamma sai na iske wani gida makwautan juna suna fada tsakaninsu, fada yayi tsanani anata zage-zage da maganganu marasa dadinji, kusan duk kunnuwansu sun toshe basa jin hakurin da ake basu, can kawai wata budurwa, dake daya daga cikin gidan makwautan, wadda bata wuce shekaru ashirinba ta koma gefe ta kira waya, ba'a jimaba sai ga sojoji sunzo suka kama matar dayan gidan da danta suka tafi dasu, amma sun dawo dasu bayan wasu 'yan awanni.

Na karshe shine, akwai wata 'yar uwata wadda sunada wata kungiya ta sa kai wadda ke sulhunta rikice-rikice tsakanin al'umma, itama take ban labarin wani rikici daya faru da wata mata da wani abokin kasuwancinta, matar tana da saurayi soja, ta kirashi yazo ya wulakanta abokin fadannata, da bincike yayi bincike aka nemo sonjan da abin ya faru dashi, dadai ya karyata labarin daga baya yace eh budurwar tashice ta hadashi da mutumin, haka aka suluntasu sojan yayi rokon kada a daga maganar, shi kuma wancan mutumin an cuceshi.

Gaskiya indai irin wannan zaici gaba da faruwa a tsakanin al'umma to tabbas sojoji zasu rasa martabar da mutane ke ganinsu da ita, soja yayi aikinshi na soja, ba shiga cikin fadan mutanen gari ba da bai wuce 'yan sanda su sasantashiba, sannan kuma aki yiwa mutum adalci, saboda bashi da kowa. Allah yasa yakai kunnen masu gyara su gyara. 

No comments:

Post a Comment