Thursday, 3 August 2017

Yaro dan shekaru goma ya tuka jirgin sama

Wani yaro me shekaru goma da haihuwa ya tuka jirgin saman fasinja a kasar Aljeriya, yaron wanda marayane yana da burin ganin ya tuka jirgin sama a rayuwarshi, hakan yasa aka kaishi gurin wasu matuka jirgin saman su biyu a yayinda jirgin ke cike makil da fasinjoji sun jira a tashi, nan kuwa daya daga cikin matukan ya tashi yaba yaron kujera ya dare ya fara tafiya da jirgin a yayinda su kuma matukan suke kula da abinda yaron yakeyi.

Yaron dai bai tashi da jirgin sama ba, yadaiyi tafiya dashine a kasa kamin daga bisani matukan jirgin su amshi ragamar tukin, saidai wannan abu da matukan jirgin sukayi yajawo an dakatar dasu daga aikinsu, yanzu haka ana tuhumarsu da sakaci da aikinsu da kuma saka rayuwar mutane cikin hadari. 

No comments:

Post a Comment