Wednesday, 13 September 2017

"A daina min kallon 'yar iska Tsoron Allah a zuciya yake">>Rahama Sadau

A hirar da tayi da jaridar The Guardian korarriyar jarumar Fim din Hausa Rahama Sadau ta tabo batutuwa da yawa da suka shafi sana'arta wanda suka hada da:

  • Rungumar da tayiwa mawaki Classiq wanda yayi sanadiyyar korarta tace duk cikin aikine.
  • Idonta ya kara budewa dalilin korarta da akayi daga finafinan hausa.
  • Anso tayi findin madigo a kudu amma ta kiya saboda kare al'ada da addininta
  • Rahama tace mutane su daina mata kallon 'yar iska dan shi tsoron Allah a zuciya yake.
Ga yanda cikakken labarin yake:

Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la'akari da daga inda ta fito watau arewa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la'akari da daga inda ta taso da kuma martaba al'ada da addinin yankin arewa.

da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damammaki na gudanar da sana'arta a dukkan fadin duniya.

Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon 'yar iska don kawai tana sana'ar ta.
naij.com

No comments:

Post a Comment