Thursday, 28 September 2017

Abubuwan da har yanzu mata ba su da izinin yi a kasar Saudiyya

Matan Saudiyya
Sarkin Saudiyya ya zartar da dokar da ta amince wa mata yin tukin mota, abin da ya kawo karshen bambancin da ake nuna wa, yayin da ita kadai ce kasar da ta haramta wa mata tuka mota a duniya.
Sai dai duk da cewa sai a watan Yunin badi ne dokar za ta fara aiki, amma kuma akwai abubuwa da dama da mata ba za su iya samu ba, a kasar da ke bin tsattsauran ra'ayin addinin musulunci.


Har yanzu dai akwai abubuwa da dama da sai mata sun nemi izinin maza kafin su aiwatar.
Wadannan abubuwa sun hada da:
  • Neman takardun yin tafiye-tafiye ko fasfo
  • Yin balaguro zuwa wasu kasashe
  • Yin aure ko neman saki
  • Bude asusun ajiya a banki
  • Idan za su fara wata harka ta kasuwanci
  • Idan za a yi musu aikin tiyata amma ba na gaggawa ba
  • Idan za su bar gidan kaso

Matan Saudiyya
Wadannan ka'idojin dai, na tasiri ne a karkashin tsarin muharami na Saudiyya.
Tun bayan kafuwarta, kasar ta ke bin tafarkin addinin musulunci na masu tsattsauran ra'ayi - wahhabism.
Bayan boren da masu tsananin kishin Islama suka yi a 1979, aka sake karfafa ka'idojin.
A cewar wani rahoto na shirin tattalin arziki na duniya na 2016, tsarin ya taimaka wajen sa kasar ta zamo daya daga cikin kasashen da ke nuna bambanci tsakanin jinsuna a Gabas ta Tsakiya, tana gaban Yemen da Syria, wadanda kasashe ne da ake yaki.
Sai dai duk da haka, akwai wasu fannoni na rayuwar mata da ba a shinfida musu ka'idoji ba, fiye da yada ake tsammani.
Tun a shekarar 2015 ne mata suka samu damar kada kuri'a.
Ilimin boko wajibi ne ga yara mata da kuma maza, har sai sun kai shekara 15, kuma an fi samun mata da suka kammala karatun jami'a a kan maza.
Kusan 16% na ma'aikatan kwadago mata ne.
Ana bukatar mata a Saudiyya su saka abaya mai tsawo, wadanda ba su kama jiki ba, a wuraren da za su yi tozali da maza wadanda ba danginsu ba ne.
Sai dai akwai wasu, da wannan doka ba ta tasiri a kansu.
An yi wa matan da suka fito daga kasashen waje sassauci game da irin rigunan da za su saka, kuma idan ba musulmai ba ne an amincesu su bar gashinsu a bude.
Wasu mata da suka fito daga kasashen ketare da suka yi tattaki zuwa kasar, sun ce sai da suka saka abaya kafin suka bar filin jirgin sama.
Amma kuma an samu matan shugabannin kasashen waje da suka kai ziyara Saudiyyar, wadanda ba su saka abaya ko kuma suka rufe gashinsu ba.
Melania Trump in a safari dress and Michelle Obama in a dress and jacketImage copyright
Kasashe kalilan ne suke amfani da dokoki da suka fayyace abubuwan da mata za su iya yi da wanda kuma ba za su iya yi ba, sai dai kuma akwai wasu wurare da aka haramta wa mata yin wasu abubuwa.
Ga wasu daga cikinsu:
China: Ma'aikatar ilimi ta China ta hana mata neman ilimin hakar ma'adinai, da na aikin gina hanyar da jirgin kasa yake bi ta karkashin kasa ko ruwa da kuma wasu darussa.
Ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsaron lafiyar mata.
Isra'ila: A Israila mata ba za su iya neman saki daga wurin mazajensu ba, saboda kotunan addini ne suke da hurumin yin haka.
A shari'ar da ba kasafai ake gani ba, alkalai a Birtaniya sun fada wa wata matar da ta nemi rabuwa da mijinta cewa hakarta ba zata cimma ruwa ba saboda mijinta ba ya son rabuwa da ita.
Rasha: Akwai wasu ayyuka da aka haramtawa mata a Rasha, ciki har da na kafinta da na aikin kwana-kwana da tuka jirgin kasa da kuma jirgin ruwa.
Indonesia: Haka kuma an haramta wa mata da ke wani gari a Indonesia zama a bayan maza a kan babur.
Magajin garin Lhoksuemawe ya bukaci mata su dinga zama a gefen babur domin kare dabi'un al'umma masu kyau.
A baya ma sai da hukumomin garin suka haramta wa mata saka wanduna masu kama jiki.
Sudan: A Sudan kuwa, hukuncin da ake yanke wa mata da suka saka wando shi ne bulala.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment