Friday, 15 September 2017

Allah yayiwa Lilamir rasuwa

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah yayiwa matashin mawakin Hiphop na Hausa, Amir Hassan wanda akafi sani da lilamir rasuwa, Rasuwa wannan matashi ta razana mutane sosai musamman wadanda suka sanshi a zahiri, abokai da 'yan uwa da masoya sai addu'ar nemamasa gafara sukeyi. Muna fatan Allah yakai rahama kabarinshi yasa ya huta. Amin.Marubuciya kuma me gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arewa24 Fauziyya D. Sulaiman tace jiyajiyannan tana tare dashi suna hira ashe yaune zai bar Duniya.

Ga abinda ta rubuta a dandalinta na sada zumunta.

"fauziyya_d_sulaimanYanzu na ke samun rasuwar Lil Amir jiya zan yi recording a Arewa24 ya shigo studio na ce masa yaka nan mu yi hoto yarana na son ka wai waye ke rubuta maka waka mamana ce ko.? Ya ce min da itace amman yanxu da kaina na ke yi, muka yi hira da shi da hoto ashe yau yaron nan zai bar duniyar, innalillahi wainna ilaihirajiun, wannan duniya ba komai bace, mutuwar matasa na girgizani."

Allah ja jikan likamir.

No comments:

Post a Comment