Friday, 15 September 2017

An daura auren dan tshohon gwamnan jihar Zamfara Abba Sani Yariman Bakura

A yau Juma'ane aka daura auren dan tshohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Sani Yariman Bakura me suna Abba da matarshi Khadija a garin Kano, Manyan mutane da suka hada da Gwamnan juhar Kano Abdullahi Umar Ganduje da na Kebbi Atiku Bagudu dana Zamfara Adbulaziz Yari dana Sakkwato Aminu Tambuwal da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da tsohon gwamnan Maiduguri Madu Sharif dadai sauransu sun halarci wannan daurin aure.Anyi kasai tacciyar walima dan wannan rana kima anci ansha an goge wuya.


Ango da amarya suma sunsha hotuna na musamman domin murnar wannan rana ta farin ciki.


Andai yi tsegume tsegume kala-kala akan shagalin wannan biki wanda suka hada da yanda amaryar da ango suka dauki hotunan kamin biki wanda angon ya rike hannun amaryar da kuma hakan ya jawo surutai da kuma maganar takalmin amaryar da aka gani me dan karaen tsada wanda shima akayita magana akanshi.

Yau dai an daura, Muna musu fatan alheri da kuma Allah ya kore dukkan sharrin shedan

No comments:

Post a Comment