Tuesday, 12 September 2017

An hana sarkin Zazzau shiga gurin taron bude kamfanin Olam da akayi a Kaduna saidai komawa gida yayi

Related image
Dazu da rana wajan taron bude katafaren kamfanin Kyankyashe kaji da yin abincin su daya faru a jihar Kaduna wanda ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan mutane an samu wani abu daya zama abin cece-ku-ce tsakanin mutane har bayan taron, abin kuwa daya faru shine hana me martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris shiga gurin taron da jami'an tsaro sukayi, sarkin yazo tare da tawagarshi sai aka dakatar dasu aka bukaci cewa sai an tantancesu sannan daga baya jami'an tsaron suka bukaci cewa wasu daga cikin dogarawan sarkin bazasu shiga cikin gurin taron ba saidai shi sarkin da wasu 'yan kadan na kusa dashi su shiga.Hakan yasa sarkin ya fasa shiga gurin taron ya juya da tawagarshi ya koma gida.

Mutane sunyi ta fadin cewa gaskiya wannan abu da aka yiwa sarkin Zazzau be daceba wanda kuma mafi yawanci aka dora laifin akan gwamnatin jihar kaduna, mutane sun rika fadin cewa ai koda ganin tawagar sarkin Zazzau be kamata ace an tsayar dasu ba, wasuma cewa suka rikayi an fifita mawaka akan sarkin Zazzau din tunda su Dauda Kahutu Rarara sun shiga gurin.

Saidai da yake mayar da martani akan wannan batu me baiwa gwamnan jihar kaduna shawara ta fannin matasa Auwal yaro me kyau ya bayyanawa manema labari cewa yawancin labarin mutane sunyita karamai gishine, amma ainihin abinda ya faru shine lokacin da sarkin Zazzau yazo shiga gurin taron dayake kofa dayace to akwai mutane sunyi dandazo a bakin shiga gurin sunata turereniyar kokarin shiga shine jami'an tsaro sukace adan dakata mutane su ragu kamin motar me martaba ta shiga, to ana cikin hakane sai tawagar maimartaba ta juya ta koma gida.

Auwal Yaro mekyau ya kara da cewa kuma jami'an tsaron dake bakin kofar shiga gurin bana gwamnatin jihar Kaduna bane na gwamnatin tarayyane shiyasa suke tantance mutane kamin su shiga gurin saboda tsaro.

No comments:

Post a Comment