Wednesday, 6 September 2017

An saka rayuwarsu cikin kunci da tagayyara saboda sunce musuluncine addininsu

Musulman kasar Myanmar kenan 'yan kabilar Rohingya da rayuwarsu ta shiga cikin tagayyara saboda irin cin mutuncin da kisan kiyashi da ake musu a kasar ta Myanmar, ana musu kisan kiyashi an kwace 'yancinsu na zama 'yan kasa wannan yasa dole suke tafiya kasashe makwauta domin neman mafaka, Andai soki gwamnatin kasar ta Myanmar da kin yin Allah wadai da wannan tozarci da akewa musulman Rohingya ballantanama su dauki wani mataki na zahiri wajan kawo karshenshi.Wannan ne yasa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira shugaban kasar ta Myanmar ko kuma Burma ya tambayi ba'asin abinda ke faruwa da kuma dalilin dayasa gwamnati bata dauki wani mataki akai ba. Shugabar kasar Aung San Suu kyi ta bayyanawa Erdogan cewa Mafi yawancin labaran da ake yadawa akan wannan rikici na karyane wasu 'yan ta'adane suke amfani da wannan dama domin kare muradunsu.

Amma gwamnatinta ta fara daukar matakan da suka dace wajen ganin an kare hakkin dukkan mutanen dake jihar Rakhine wanda anan ne kabilar 'yan Rohingyar suke, haka kuma ta kara da cewa tasan abin da ciwo a tauyewa mutum 'yancinshi na walwala da yin rayuwa kamar kowa amma gwamnatinta tana kokarin ganin ta dawowa da mutanen yankin 'yancinsu, amma ta kara jaddada cewa tabbas mafi yawancin labarai da hotunan da ake yadawa na bogine, wasu 'yan ta'addane ke kokarin yayata manufofinsu.
Manyan kafaen labarai na Duniya, irin su BBC da Aljazera da Reuters harda ma majalisar dinkin Duniya sun ruwaito irin yanda azabtar da wadannan bayin Allah yasa suke tafiya a kasa dan yin gudun hijira mafi yawanci cikin kasar Bangladesh, yawanci kananan yara ne da mata da tsofaffi suke tafiya cikin tabo da ruwa da daji da iska domin su samu su tsira da rayuwarsu.

Haka kuma rahotanni sunce mutanen suna cikin yunwa hakama 'ya 'ya yensu yawanci ciwon yunwa da rashi abinci me gina jiki ya kamasu, rahotanni dai sunce kasar Burma bata bari 'yan jarida suna shiga yankin da rikicin ke faruwa dan kar su dauki hotunan ainihin yanda lamarin yake amma akwai rahotannin cin zarafi da sojoji kewa 'yan kabilar Rohingya dake yawo kuma za'a iya fahimtar hakan ta irin yanda mutane ke barin gidajensu suna tafiya me nisan gaske a kafa, kai kasan ba lafiya zata sa haka ba.


Jama'a mu sakasu a addu'a. 

No comments:

Post a Comment