Thursday, 14 September 2017

Ana tsegumin cewa diyar shugaban kasa Zahara Buhari Indimi na dauke da juma biyu

Mutane na ta rade-radin cewa Zahra Buhari na da ciki (hotuna)

Bayan billowar wani sabon hoton yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Indimi, mutane da dama sun yanke cewar tana dauke da juna biyu. 

Ana ta rade-radin cewa Zahra Indimi wacce ta halarci taron bude gidan kwalliya na yar mataimakin shugaban kasa, Kiki Osinbajo na sauraron dan ta na fari tare da mijinta Ahmed Indimi. Wani shahararren mai daukar hoto na Najeriya ne ya dauki hoton yar shugaban kasar wanda ya janyo cece-kucen sannan an dauki hoton ne tana sanye da wani bakin dogon riga da hula da ya dace da shigar.

Sakamakon cikowar da fuskar ta tayi a cikin sabon hoton, yasa mabiyanta a shafin Instagram da dama yanke hukuncin cewa tana dauke da juna biyu.CACOL ta lissafo ministoci 4 da ya zama dole Buhari ya dakatar da su Wata matashiya tace: 

“Hahhahahhahha Zarah wannan juna biyun ya nuna a jikin ki… gwanda ma ki fara shirya mashi. Ina zamuje mu haihu? Don Allah karda kisa Amurka ciki saboda bazan je chan ba.” 

Ga sharhin da mutane suka yi a kai:

Mutane na ta rade-radin cewa Zahra Buhari na da ciki (hotuna)
naij.com

No comments:

Post a Comment