Tuesday, 19 September 2017

Babu maraya sai raggo: Kalli abubuwan da tayi da kafarta duk da cewa bata da hannaye

Allah sarki rayuwa nakasa ba tana nufin mutum ya zama nauyi akan mutane ba ko kuma ya kashe zuciyarshi ya rika bara da neman komai sai an yi mishi ba, wannan wata baiwar Allahce da bata da hannaye biyu amma gashi ta iya saka kayan sawa da kafarta, duka wadannan kayan sawar na yara da ake iya gani a kusa da matar a wannan hoto itace ta sakasu da kafarta.Lallai kam babu maraya sai raggo.

No comments:

Post a Comment