Friday, 22 September 2017

"Baki da da'a kwata-kwata kuma a haka babu mutumin kirki dazai fito neman aurenki">>wani ya gayawa Hadiza Gabon

Ba sabon labari bane ga masu bibiyar abubuwan dake wakana a shafukan sada zumunta akai-akaiba cewa wani bawan Allah ya kure hakurin Fitacciyar Jarumar fim din Hausa Hadiza gabon  ba, a yayin daya mata magana a dandalinta na sada zumunta cewa ta  girma ya kamata tayi aure,  cikin bacin rai Hadizar ta mayar mishi da martanin da yaja hankulan mutane sosai.Hadizar tacemai toh ko zaiwa mahaifinshi magana ya saki mahaifiyarshi sai ya aureta?
 Gadai hoton yanda abin ya kasance kamar haka:
A binciken da shafin hutudole.com yayi ya gano cewa mafi yawan wadanda sukayi sharhi akan wannan magana ta Hadiza da wannan bawan Allah me suna M. Bash sun bayyana cewa bai kamata Hadizar ta fadi irin wannan magana ba lura da cewa ita sananniyar mutumce maganar tayi tsauri da yawa.

Wani daga cikin wadanda sukayi sharhi ya rubuta da harshen turanci cewa " Gaskiya baki da dabi'a kwata-kwata kuma da irin wannan maganar da kikayi babu mutumin kirki dazai fito neman aurenki."

Da yawa dai sun bayyana Hadiza da me hakuri amma basusan yanda akayi hakan ya faruba.
Gadai sauran ra'ayoyin mutane dangane da wannan lamari.
Allah ya kyauta.

No comments:

Post a Comment