Tuesday, 12 September 2017

"Bana yiwa Ali Nuhu zagon kasa, Hassadace ke damun wasu masoyanshi akaina">>Rahama Sadau

A karshen makon daya gabatane aka samu wani fadan cacar baki tsakanin magoya bayan Babban jarumin fim din Hausa Ali Nuhu  (Sarki) dana Jaruma Rahama Sadau wadda shi Ali Nuhunne ya kawota masana'antar finafinan Hausa, Magoya bayan Ali Nuhu sun zargi Rahama da yin kalaman batanci da kuma zagon kasa ga Ali Nuhu, fadan yayi zafi sosai yanda magoya bayan Ali Nuhu suka rika jifar Rahama Sadau da munanan kalamai, amma daga baya sukace komai ya wuce.Tun wancan lokaci ba'aji wani tsakanin Ali ko Rahama yace uffan dangane da wannan fada ba, sai yau shafinnan na Kannywood exclusive yace yayi hira da Rahama Sadau akan fadan daya faru kuma ta bayyana musu cewa zargin da masoyan Ali Nuhun suke mata babu gaskiya a cikinshi kawai dai suna mata hassadane bisa daukakar data samu

Gadai labarin da Kannywoodexclusive suka wallafa a shafinsu.

"Jaruma Rahama Sadau ta musanta zargin da wasu magoya bayan Ali Nuhu suke mata na cewa tana yi wa jarumin zagon kasa a wasu hirarraki da ta ke yi.

A wata tattaunawa da mu ka yi da jarumar kai tsaye, jarumar ta ce wannan ba komai ba ne illa hassada da magoya bayan Ali Nuhu suka nuna mata domin irin nasarorin da take ta samu a rayuwa."

No comments:

Post a Comment