Friday, 15 September 2017

"Burina in haddace kur'ani amma an kashemin babana na kuma zama 'yar gudun hijira daga kasar Burma">>inji yarinya 'yar shekaru 10

Wannan yarinyar ta sama sunanta Noor Kajol kamar yanda ta gayawa kafar watsa labarai ta Aljazeera kuma shekarunta Goma da haihuwa, ta fitone daga kasar Burma ko kuma Myanmar inda ake cin mutuncin da kisan kabilar musulmai ta Rohingya, yarinyar tace suna tare da babanta a cikin gida sai sojoji suka yo harbin bindiga ya shigo ta kofar taga ya samu babanta akai.Yarinyar tace babanta ya fadi kasa cikin jini haka kuma sojojin suka bankawa gidansu wuta wanda delo tasa suka gudu ita da mahaifiyarta, tace gawar babanta a cikin gidan ta kone, yarinyar ta kara da cewa tana zuwa makarantar Isilamiya tana koyon karatun alkurani kuma burinta shine ta haddace kur'ani. Amma gashi yanzu tabar garinsu inda take so an rabata da babanta wanda har yanzu tana kewarshi.

Tafiyar kwanaki uku sukayi a kasa kamar yanda yarinyar ta fada kamin sukai kasar Bangladesh inda suka zama 'yan gudun hijira, yarinyar tace batason gurin da aka ajiyesu domin babu gurin bahaya kuma babu gurin wanka kuma kazanta tayi yawa a gurin.

A karshe tayi kira ga al'ummar Duniya dasu taimaka a mayar dasu kasarsu ko kuma a samamusu wata kasa da zata amshesu a matsayin mutane 'yan kasa masu 'yanci

No comments:

Post a Comment