Tuesday, 12 September 2017

"Dan malam yaki halin Malam": Hotunan kamin biki na dan tsohon gwamnan Zamfara Alhaji Sani Yariman Bakura sun jawo cece-ku-ce

Wadannan hotunan kamin bikine na dan gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sani Yariman bakura sun jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara, Alhaji Abba Ahmad Rufa'i Sani da amaryarshi Hajiya Khadija Danlami Alhassan Iman sun dauki irin hotunan nan ne da akeyi kamin ranar Daurin aure wanda ake nunawa abokai na 'yan uwa cewa ranar aurenmu ta kusa fa, Ranar juma'a me zuwa idan Allah ya kaimu 15 ga watannan na Satumba za'a daura aurennasu, kuma Abba ya rike hannu da jikin Khadija a cikin hotunan nasu, wannanne yasa mutane suka rika fadin dan "Malam yaki halin Malam" ganin cewa mahaifinshine ya fara kawo maganar kafa shari'ar musulunci a gwamnatance a Najeriya.Wasu kuma sun rika fadin tunda dai zamanine yazo da haka basuga wani abin magana ba a cikin wadannan hotunan da aka dauka.
No comments:

Post a Comment