Wednesday, 13 September 2017

Diyar Ali Nuhu, Fatima an zama 'yanmata

Jarumar fim din Hausa kuma diyar babban Jarumi Ali Nuhu wato Fatima kenan a wannan hoton, tasha kyau sosai, ta girma ta zama 'yan mata, cikakkiyar Budurwa, son kowa kin wanda ya rasa, Mahaifin nata Ali Nuhune ya saka hotonnan nata a dandalinshi na sada zumunta ina ya rubuta "Diyata".Mutane da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoton na Fatima Ali Nuhu sun yabashi sannan suka mata fatan alheri.

Saidai an samu wani bawan Allah daya yiwa Ali Nuhun habaici wanda kuma hankalin mutane ya koma kanshi wasuma har raddi suka rika yi mishi da cewa abinda ya fadi be kamata ba.

Mutumin dai ya rubuta cewa" Kaga itama(Fatima) ta ga jeka(Ali Nuhu) da rawa da tsalle-tsalle. Sha sha sha".
No comments:

Post a Comment