Tuesday, 26 September 2017

Dubai ta kaddamar da mota me tashi sama ta farko a Duniya

Garin Dubai ya kaddamar da mota me tashi sama ta farko a Duniya a jiya Litinin, motar me daukar mutum biyu kacal bata da bukatar matuki, kuma itace irinta ta Farko da aka fara amfani da ita a wani birni na Duniya.Wani kamfanin kasar Jamusne dake kera jirage marasa matuki suka kera motocin, kuma hukumomin garin Dubaidin sunce an kera wadannan motocinne dan kara sauwakewa mutane harkar zirga-zirgar cikin gari da kuma saka farinciki a zukatansu.

No comments:

Post a Comment