Sunday, 24 September 2017

Duka goma da duk karfinka bazaka iya ramawaba

Image result for stroke of a whip
Watakila zakayi mamakin cewa akwai dukan da za'ayimaka wanda duk karfinka bazaka iya ramashiba koda kuwa kana da ikon yin hakan, suna da yawa amma ga  guda goma mafi shahara da muka zakulo muku:

1. Dukan Ruwan Sama.

2. Dukan Jami'an tsaro.

3. Kana kallon kwallo a dokota ta bigeka.

4. Yin tuntube ko bugewa da wani abu marar motsi.

5. Dukan malaminka idan kana da tarbiyya bazaka ramaba.6.Dukan iyayenka idan kana da tarbiyya da son gamawa lafiya bazaka tamaba.

7.Dukan wanka idan kana da tarbiyya bazaka ramaba.

8.Dukan masoyiyarka a lokacin da kuke cikin wasa, irin kadan tsokaneta dinnan ta kawo maka duka cikin wasa.

9. Wanda yafi karfinka idan ya bugeka saidai kayi Allah ya isa.

10. Dukan hukuma, hukunci, idan hukuma tasa a maka bulala a matsayin hukunci ko bakar magana baka isa kayiba.

Kasan wani dukan da idan akawa mutum bazai iya ramawaba? Fada a cikin comment.

No comments:

Post a Comment