Tuesday, 5 September 2017

"Duniya ko ina akwai kama karya">> Wani yayi nuni da yanda Shugaba Buhari yake fifita 'ya 'yan A'isha akan na tsohuwar matarshi Safina

Wani bawan Allah me suna Abdullahi A. Abdullahi yayi nuni da irin yanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jan 'ya 'yan matarshi ta yanzu, A'isha a jiki fiye da yanda yake jan 'ya 'yan tshohuwar matarshi, Safina da ta rasu.

Abdullahi ya rubuta a dandalinshi na sada zumunta da muhawar kamar haka"Kamar yanda muke da sarki me daraja ta daya dame daraja ta biyu, koda a cikin 'ya 'yan shugaban kasa akwai 'ya 'ya masu daraja ta daya da masu daraja ta biyu.


Yaci gaba da cewa "ya yan A'isha sune masu daraja ta daya a gurin shugaba Buhari, 'ya 'yan marigayiya tsohuwar matar shugaban kasa, Hajiya Safina sune 'ya 'ya masu daraja ta biyu,

Abdullahi ya kare zancenshi da cewa "Duniya ko ina akwai kama karya fah"

A cikin bikin sallar daya gabatane diyar Shugaban kasa, Zahara Buhari ta saka wannan hoton na 'yan gidansu daya ja hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta da muhawara to saidai babu 'ya 'yan marigayiya Safina a cikin hoton watakila shiyasa wannan bawan Allah yayi wannan rubutu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Safina sun rabu a matsayin mata da miji kamin ta rasu a cikin wani labari mai sarkakkiyar gaske wanda ba'a san aini gaskiyar me ya faruba.

No comments:

Post a Comment