Sunday, 10 September 2017

Fadan cacar baki tsakanin masoyan Ali Nuhu da Rahama Sadau ya kare: Amma ya fito da wani abu fili

Fadan cacar baki tsakanin 'yan Gani kashenin masoyan babban Jarumin fim din hausa, Ali Nuhu da  na korarriyar jaruma Rahama Sadau ya kare, domin kuwa wadanda suke gaba-gaba a fadan sun fito sunce komi ya wuce kuma dukkan sakonnin zage-zage dana batanci da suka gayawa junansu a dandalinsu na sada zumunta sun gogesu.


To saidai masu sharhi akan wannan lamari sun bayyana ra'ayoyi da cewa fadan ya fito da wani abu fili da mutane ke kokwanton shi da kuma zargin musamman 'yan matan fim din hausa dashi, a cikin sakonnin masoyan Ali Nuhu da suka rubuta suna zagin Rahama Sadau da cimata mutunci sun rika kiranta da Karuwa da sauran munanan kalamai masu nauyin fadi.

Mutane da dama nawa matan fim din Hausa kallan wadanda basu da tarbiyya to sai ga abokan huldarsu da suke yin finafinai tare suna jifan junansu da kalaman fatanci saboda bacin rai da kuma rashin fahimta data shiga tsakani, tonon sililidai bashi da amfani domin yana tono abinda ba'ason ji.

Allah shi kyauta. 


No comments:

Post a Comment