Monday, 25 September 2017

Farfesa Attahiru Jega abin alfaharin Arewa da Najeriya

Tshohon shugaban hukumar zabe ta kasa farfesa Attahiru Jega kenan wanda a karkashinshine aka bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari zababben shugaban kasarnan aka kuma kada shugaban kasa na kan mulki, duk da baraza kala-kala amma duk ya shanye yayi abinda ya kamata, idan zamu iya tunawa a lokacin da ake karba da bayyana sakamakon zabe daga jihohin Najeriya wani me suna Orubebe ya dan taba wani haukan karya a lokacin da ya ga cewa jam'iyyarshi ta PDP da ubangidanshi sun dauki hanyar shan kasa.Har ya tashi yayi zarge-zarge marasa tushe da kuma bakaken maganganu na nuna kabilanci ga farfesa Jega, saida Jega ya barshi ya gama sannan ya mayar mishi da martani irin na mutane masu dattako, Jega ya tabbatarwa mutane da cewa shi cikakken farfesane kuma yana amfani da iliminshi kuma ya fito daga yankin mutane masu mutunci bazamu taba mantawa da gudumuwar daya bayarba.

Munawa Farfesa Jega fatan alheri da fatan Allah ya kara tsareshi da kara daukaka.

No comments:

Post a Comment