Monday, 11 September 2017

Ganawar shugaban kasa M. Buhari da majalisar sarakunan Gargajiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinshi farefesa Yemi Osinbajo sun karbi bakuncin majalisar masu rike da sarautun gargajiya yau a Fadar shugaban kasar dake Abuja, shugaban ya tattauna batutuwa da dama a taron nasu, wani bayani hda yayi da yafi daukar hankalin mutane a gurin taron shine cewa yaji dadi da daminar bana tayi albarka aka samu albarkar kayan gona wannan yana nuna cewa Allah ya amsa addu'ar talakawan Najeriya.


 Shugaba Buhari yayi wani barkwanci a gurin taron inda yake cewa har ya fara tunanin kasar da zai tafi gudun hijira da ace damunar bana batayi kyauba
Allah ya kara taimakonmu da shuwagabanninmu masu nufinmu da alheri.No comments:

Post a Comment