Friday, 15 September 2017

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yana bi cikin layukan garin Kaduna dan fadakar da mutane akan muhaimmancin zaman lafiya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai kenan a yau juma'a ya shiga cikin gari cikin layuka yana jawo hankulan mutane da kuma fadar dasu akan muhimmancin zaman lafiya, mutane sun yaba da wannan yunkuri nashi, andai samu wasu bata gari suna yayata cewa wai ana fada a garin Kaduna wanda hakan karyace tsagoronta, gwamnan yayi kira da mutane da a zauna lafiya, kuma ya dauki matakan tsaro dan ganin cewa ba'a samu wani hargitsiba.

No comments:

Post a Comment